Isa ga babban shafi
Amurka

"Za mu ci gaba da mutunta yarjejeniyar nukiliyar Iran"

Manyan kasashen duniya sun mayar da martani ga shugaban Amurka Donald Trump, in da suka ce za su ci gaba da mutunta yarjejeniyar nukiliyar Iran bayan ya  barazanr kekketa ta.

Shugaban Amurka Donald Trump ya yi barazanar keta yarjejeniyar nukiliyar Iran
Shugaban Amurka Donald Trump ya yi barazanar keta yarjejeniyar nukiliyar Iran REUTERS/Kevin Lamarque
Talla

A wani kakkausan jawabi da ya gabatar a fadar White House, Mr. Trump ya caccaki yarjejeniyar wadda ta samu goyon bayan kasashen Birtaniya da Faransa da Jamus da Rasha da kuma kungiyar Tarayyar Turai.

Manyan kasashen sun ce, yarjejeniyar wani bangare ne na tabbatar da tsaro a kasashensu kuma za su ci gaba da mutunta ta.

Mr. Trump ya zargi Iran da tallafa wa ayyukan ta’addanci a yankin gabas ta tsakiya, yayin da ya bukaci sake kakaba wa kasar takunkumi.

A cewar Trump, tuni Iran ta karya ka’idojin yarjejeniyar nukiliyar da aka kulla a shekarar 2015, amma hukumar da ke sanya ido kan makamnin nukiliya ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce, Iran na mutunta sharuddan da aka gindaya ma ta.

A wani jawabinsa da aka watsa ta kafar talabijin a ranar jumma’a, shugaban Iran Hassan Rouhani ya ce, suna mutunta sharuddan yarjejeniyar, in da ya zargi Trump da furta kalamai mara tushe.

Tuni kasashen Isra’ila da Saudiya suka yi madalla da matakin da Trump ya dauka.

Yanzu haka dai, Majalisar Dokokin Amurka na da kwanaki 60 don yanke shawarar janyewa daga yarjejeniyar ta hanyar sake kakaba takunkumi ga Iran bayan Trump ya ki sanya hannun da zai tabbatar wa Majalisar cewa, ya gamsu cewa, Iran na mutunta sharuddan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.