Isa ga babban shafi
Korea ta Arewa- China

Korea ta Arewa ta dakatar da kera makamin nukiliya- Jong Un

Shugaban Korea ta Arewa, Kim Jong Un ya tabbatar wa takwaransa na China Xi Jinping cewa kasarsa ta ajiye batun kera makaman Nukiliyar da ta ke yi.Kim wanda ke sanar da hakan yayin wata ziyarar sirri da ya kai Beijing ya ce, alaka tsakaninsa da China za ta ci gaba da dorewa ko da bayan gyara tsakaninsa da Amurka.

Shugaban Korea ta Arewa  Kim Jong Un tare da matarsa Ri Sol Ju a fadar shugaban China Xi Jinping da mai dakinsa a tare da su
Shugaban Korea ta Arewa Kim Jong Un tare da matarsa Ri Sol Ju a fadar shugaban China Xi Jinping da mai dakinsa a tare da su Reuters/路透社
Talla

Ziyarar a China ita ce irinta ta farko da shugaba Kim ya kai wata kasa tun bayan fara mulkin kasarsa a shekarar 2011, in da ya tabbatar wa Xi jinping cewa a shirye ya ke ya tattauna da shugaba Trump na Amurka da takwaransa na Korea ta Kudu Moon Jae-in.

Shugaba Kim Jong Un wanda ya kai ziyarar tare da rakiyar mai dakinsa Ri Sol-ju ya samu kyakkyawar tarba daga takwaransa na China Xi Jinping.

Yayin tattaunawarsu, Kim ya ce ajiye shirin harhada makaman nukiliyarsa zai yi aiki ne kadai idan Amurka da Korea ta Kudu suka yi maraba da matakin tare da kawo karshen takaddamar da ke tsakaninsu da kuma wanzar da zaman lafiya.

Tuni dai shugaban Amurka Donald Trump ya yi maraba da matakin, sai dai ya ce, ba cikin gaggawa za a janye takunkuman da aka sanya wa Korea ta Arewan ba, har sai an tabbatar da sauya takunta.

Kasashen Korea ta Arewa da China dai na kokarin ganin sun kara kyautata alakar da ke tsakaninsu ne gabanin sasantawa da Amurka da kuma Korea ta Arewa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.