Isa ga babban shafi
Amurka

Trump ya shirya tattaunawa da shugaban Korea ta Arewa

Shugaban Amurka Donald Trump ya nada babban jami’in leken asirinsa don tallata manufarsa ta shiga tattaunawa da shugaban Korea Ta Arewa, Kim Jong Un kan makamin nukiliya.Tuni Trump ya yi hasashen yiwuwar gudanar da wannan tattaunawa mai cike da tarihi, yayin da wasu manazarta siyasa ke bayyana fargabarsu kan lamarin.

Shugaban Korea ta Arewa Kim Jong Un da shugaban Amurka Donald Trump
Shugaban Korea ta Arewa Kim Jong Un da shugaban Amurka Donald Trump AFP
Talla

Direktan Hukumar Leken Asirin Amurka ta CIA, Mike Pompeo ya bayyana Korea ta Arewa a matsayin kasar da ta kintsa tattaunawa sakamakon matsin lambar da ta sha na kakaba ma ta takunkumai karkashin jagorancin Amurka.

Pompeo ya shaida wa manema labarai cewa, ba su taba samun labari kan kuncin da tattalin arzikin Korea ta Arewa ya shiga ba kamar wannan lokaci.

Sai dai jami’in ya ce, kawo yanzu babu wata matsaya da bangarorin biyu suka cimma a tsakaninsu, yayin da shugaban na Amurka Donald Trump ya fito karara ya bayyana aniyarsa ta zaman sulhu da Kim Jong Un.

"Idan zai bari ganawar ta kasance, to ya kamata mu kyautata, bari dai mu ga abin da zai faru, ko dai a yi wannan ganawa ko kuma a’a babu dai wanda ke da masaniya." in jin Trump.

shugaban ya kara da cewa, za su iya zaman tattaunawa don cimma muhimmiyar yarjejeniya ga duniya, da kuma kasashen Amurka da Korea ta Arewa.

Manazarta siyasar Amurka na ganin akwai tarin hatsurra a wannan ganawa tsakanin kasashen biyu da ke tunkawo da karfin makamin nukiliya, musamman idan tattaunawar ta sukurkuce

Ko da dai Pompeo ya ce, Trump ya fahimci hatsurran da ke ciki, kuma zai magance matsalar.

Kawo yanzu dai babu wani shugaban Amurka da ya taba zaman tattaunawar keke da keke da shugaban Korea ta Arewa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.