Isa ga babban shafi
Afghanistan

An kai harin kunar bakin wake a hukumar zaben birnin Kabul

Akalla mutane 31 sun rasa rayukansu bayan wani harin kunar bakin wake da aka kai hukumar zaben Kabul na kasar Afghanistan a yau lahadi,yayinda  mutane 54 suka jikata.

Harin kunar bakin wake a hukumar zaben birnin Kabul na kasar Afghanistan
Harin kunar bakin wake a hukumar zaben birnin Kabul na kasar Afghanistan REUTERS/Omar Sobhani
Talla

Harin ya auku ne a birnin Kabul a dai dai lokacin da jama’a ke ci gaba da zuwa hukumar zaben Kabul wajen yi rijista dama karbar takardun zabe.

Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan Kabul Najib Danish,, ya tabbatar da mutuwar mutane 31 tare da jikkatar wasu 54.

Kawo yanzu babu wata kungiya da ta dauki alhakin kaddamar da harin na yau.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.