Iran ta sha alwashin cigaba da kasancewa cikin yarjejeniyar nukiliya
Kasar Iran ta bayyana shirinta na ci gaba da kasancewa cikin yarjejeniyar nukiliya da ke tsakaninta da kasashen yammacin Duniya ko da kasar Amurka ta fice daga cikinta.
Wallafawa ranar:
Shugaban kasar Iran Hassan Rouhani ya ce ba abinda zai hana Iran ci gaba da kasancewa cikin yarjejeniyar matukar sauran kasashen mahalarta tattaunawar basu fice ba.
A ranar Assabar mai zuwa ake sa ran shugaba Trump na Amurka zai fayyace wa Duniya matsayin kasar Amurka dangane da yarjejeniyar Nukiliyar Iran, da kasar Iran a baya ta sha nanatawa Amurka cewar za ta yi babbar nadama a tarihi matukar ta wancakalar da ita.
Tuni dai kasashen Birtaniya, China, Faransa, Jamus da Rasha suka janyo hankalin Amurka akan ta tsaya a yi da ita.
Ko a kwanan nan ma an ji shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron na neman sauran manyan kasashen Duniya da su sa baki kada yarjejeniyar ta kife, harma yana yi wa shugaba Trump kashedin cewar akwai yiwuwar barkewar yaki matukar Amurka ta yi sakacin lalacewar yarjejeniyar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu