Sabon shirin kare yarjejeniyar Nukiliyar Iran daga Turai
Kungiyar kasashen Turai ta kaddamar da wani shirin tattalin arzikin domin cigaba da kare yarjejeniyar nukiliyar Iran bayan ficewar kasar Amurka.
Wallafawa ranar:
Bayan ganawar da ministan harkokin wajen kasar Iran Muhammad Javad Zarif da wakilan kungiyar Turai a Brussels, shugabar diflomasiya Frederico Mogherini tace suna daukar matakan ganin Iran ta cigaba da sayar da mai da kuma gas din ta a kasuwannin duniya.
Mogherini tace suna kokarin ganin sun kaucewa takunkumin hada hadar kasuwancin da Amurka ta sanyawa Iran wanda ke aiki a sassan duniya.
Zarif ya bayyana shirin a matsayin matakin farko mai kyau, amma kuma Iran na bukatar tabbatar mata da bukatun da take nema.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu