Isa ga babban shafi
Amurka-korea ta Arewa

Donald Trump ya sake baiwa Koriya ta Arewa dama

Sa’oi 24 bayan sanar da janyewar sa daga batun ganawa da Shugaban Koriya ta Arewa Kim Jong Un, Shugaban Amurka Donal Trump ya bayyana cewa ya na kyautata ganawa da shugaban Koriya ta Arewa.

Shugaba Donald Trump da Kim Jong-Un
Shugaba Donald Trump da Kim Jong-Un 路透社
Talla

Shugaban na Amurka ya bayyana cewa mai yiyuwa ya gana da Kim Jong Un ranar 12 ga watan Yuni a Singapore.

A shafin na Twitter Shugaban na Amurka ya rubuta cewa tattaunawar sa da hukumomin Koriya ta Arewa ta yi nisa, a haka ya na da yekini sun samu ganawa da Shugaban Koriya ta Arewa a Singapore.

Wasikar farko da Shugaban Amurka ya aike zuwa Shugaba Kim Jong Un ta bayyana manufofin shugaban, inda yake cewa  Amurka ta yi fatan yiwuwar tattaunawar don samun zaman lafiya wadda tun farko ba ita ta nema ba, amma har yanzu kofa a bude ta ke ga Kim idan abubuwa sun nutsa.

Cikin wasikar ta Shugaba Donald Trump ya ce duk da Kim na barazana da makaman Nukiliya amma ya sani fa suna da makaman da suka fi nashi wanda kuma basa fatan amfani da shi kan kowacce kasa ko wani bil'adama.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.