Isa ga babban shafi
Iran-Amurka

Amurka ta gabatar da sharudda 12 don sabunta yarjejeniyar Iran

Kasar Amurka ta gabatar da sabbin sharidodi 12 masu tsauri domin kulla yarjejeniyar nukiliyar Iran, yayin da kasar ta yi barazanar daukar matakai masu tsauri kan kamfanonin kasashen Turai da suka cigaba da hulda da ita.

Sakataren harkokin wajen ya ce matakan da za su dauka zai nunawa shugabannin Iran cewar da gaske su ke wajen bayyana kudirorin su kan kasar.
Sakataren harkokin wajen ya ce matakan da za su dauka zai nunawa shugabannin Iran cewar da gaske su ke wajen bayyana kudirorin su kan kasar. REUTERS/Jonathan Ernst
Talla

Yayin da ya ke gabatar da sabbin manufofin Amurka kan kasar Iran, Sakataren harkokin waje Mike Pompeo ya ce zasu kakabawa Iran takunkumin karya tattalin arzikin mai karfin da ba su taba yi ba a tarihi, bayan janye kasar daga yarjeniyar nukiliyar shekarar 2015.

Pompeo da ke gabatar da jawabi kan manufofin Amurka na farko tun bayan nadin da aka masa, ya ce Amurka za ta tabbatar da dakile karfin fada ajin Iran da ke fadadawa a Gabas ta Tsakiya da kuma gindaya sharidodi 12 masu tsauri domin kulla wata sabuwar yarjejeniya.

Sakataren harkokin wajen ya ce matakan da za su dauka zai nunawa shugabannin Iran cewar da gaske su ke wajen bayyana kudirorin su kan kasar.

Tuni kasashen Turai suka bijirewa Amurkar wajen kin bin umurnin ta wajen harka da Iran da kuma sanya dokar da za ta kare kamfanonin su da ke harkokin kasuwanci a Iran.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.