Isa ga babban shafi

Jami'an diflomasiyyar EU, Rasha da China na tattaunawa akan Iran

Jami’an Diflomasiya daga nahiyar turai, China da kuma Rasha sun fara tattaunawa kan samar da wata yarjejeniya, wadda a cikinta zasu mikawa Iran taimakon kudade domin ta dakatar da shirinta na kera manyan makamai masu linzami, hadi da rage tasirinta a al’amuran diflomasiya da tsaron yankin Gabas ta Tsakiya.

Wasu 'yan kasar Iran da ke zanga-zangar kin jinin shugaban Amurka Donald Trump a birnin Teheran, bayan da ya janye daga yarjejeniyar nukiliyar Iran.
Wasu 'yan kasar Iran da ke zanga-zangar kin jinin shugaban Amurka Donald Trump a birnin Teheran, bayan da ya janye daga yarjejeniyar nukiliyar Iran. Reuters
Talla

Wani lokaci cikin makon da zamu shiga, jami’an Diflomasiyyar zasu sake haduwa a birnin Vienna domin cimma matsaya kan mataki na gaba.

Faransa, Jamus, Birtaniya, Rasha Da China zasu shiga cikin tattaunawar amma banda Amurka, yayinda babu tabbas ko Iran zata halarci taron, wadda a baya ta sha yin watsi da bukatar dakatar da shirinta na kera manyan makamai masu linzami da ke cin dogon zango.

Matakin sabon yunkuri ne na ceto yarjejeniyar nukiliyar Iran ta 2015, wadda Amurka ta fice daga cikinta a farkon watan Mayu, bayan nuna rashin gamsuwa akan yadda yarjejeniyar bata shafi shirin kera makamai masu linzami masu cin dogon zango da kasar ta Iran ke yi.

Zalika Amurka ta ce tilas yarjejeniyar ta hana Iran taimakawa wasu kungiyoyin gwagwarmaya a yankin gabas ta tsakiya, wadanda take kallo a matsayin ‘yan ta’adda.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.