Isa ga babban shafi
Saudiya

Sama da Musulmi miliyan 2 sun gudanar da tsayuwar Arfa

Sama da Musulmi miliyan biyu ne a yau Litinin, suka gudanar da tsayuwar Arfa a birnin Makkah da ke kasar Saudiya, daya daga cikin manyan ginshikan ibadar aikin Hajji.

Al'ummar Musulmi, yayin gudanar da ibadar tsayuwar Arfa yayin aikin Hajjin bana a birnin Makkah na kasar Saudiya.
Al'ummar Musulmi, yayin gudanar da ibadar tsayuwar Arfa yayin aikin Hajjin bana a birnin Makkah na kasar Saudiya. AHMAD MASOOD/REUTERS
Talla

A bana dai mahukunta a kasar Saudiyya, sun dauki tsauraran matakai musamman na tsaro domin tabbatar da cewa aikin ya gudana a cikin tsananki da kwanciyar hankali.

Tarihi ya tabbatar da cewa dutsen na Arfa, shi ne wurin da Manzon Allah Annabi Muhammad Sallallahu Alay-hi Wa-sallam, ya gabatar hudubarsa ta karshe yayin aikin Hajjin bankwana sama da shekaru 1,430 da suka gabata.

Ibadar aikin Hajji, daya ce daga cikin ginshikan addinin Musulunci guda biyar, wadda ake bukatar duk Musulmin da ya samu budi ko hali, ya gudanar da ita ko da sau daya ne a rayuwarsa, muddin yana da isasshiyar lafiya da dukiyar yin hakan.

A ranar Talata al’ummar Musulmi za su gudanar da ibadar layya, inda za’a yanka dabbobi kama daga raguna zuwa shanu ko rakuma da sauran wadanda addini ya bayarda dama, a matsayin ranar babbar Sallah, abinda ke kawo karshen ayyuka ko ibadar Hajjin bana.

Daga filin na Arfat, wakilinmu Muhammad Kabir Yusuf ya aiko mana rahoto.

02:55

Sama da Musulmi miliyan 2 sun gudanar da tsayuwar Arfa

Kabir Yusuf

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.