Isa ga babban shafi
MDD- Venezuela

MDD na taka-tsan-tsan a rikicin Venezuela

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya ce, Majalisar ba za ta shiga wata kungiyar kasashen duniya ba da ke kokarin sasanta rikicin kasar Venezuela.

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guterres
Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guterres REUTERS/Pierre Albouy
Talla

Wannan ya biyo bayan bukatar kasashen Mexico da Uruguay na gayyatar Guterres domin halartar taron da suka shirya a ranar Alhamis mai zuwa.

Yayin da yake mayar da martani ga shirin taron da kasashen suka kira domin tattauna rikicin Venezuela,  Guterres ya ce, Majalisar ta dauki matsayin kaucewa wadannan kungiyoyin kasashe saboda tabbatar da sahihancin aniyarta ta sasanta rikicin.

Tuni kasashe irin su Amurka da Faransa da Birtaniya da Jamus da Spain da Canada da Australia da kuma tarin wasu kasashen daga yankin kudancin Amurka suka bayyana goyan bayansu ga shugaban kasar Venezuela na riko, Juan Guido, yayin da kasashe irin su Rasha da China suka ki amincewa da matakin.

Rarrabuwar kawunan da aka samu ya jefa Majalisar Dinkin Duniya cikin tsaka mai wuya, wajen nuna bangaren da take goyan baya.

Suma kasashen Mexico da Uruguay sun ki amincewa da shugaban na riko.

Guterres ya ce,  yana sa ido kan abin da ke faruwa a Venezuela, bayan ganawa da Jakadan Mexico, Jose Gomez Camacho, wanda ya shaida masa cewar, taron da suke shiryawa ranar Alhamis zai bada damar tattaunawa ne tsakanin bangarorin da ke rikicin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.