Isa ga babban shafi
Isra'ila-Falasdinawa

Isra'ila ta take hakkin bil'adama a yankin Falasdinu - MDD

Majalisar Dinkin Duniya ta ce ta na da kwararan hujjoji da ke nuna yadda Isra’ila ta ci zarafi tare da take hakkin bil’adama a yankin gaza, ta yadda jami’an tsaronta suka hallaka wasu tarin jami’an lafiya da kananan yara, yayin zanga-zangar da Falasdinawa suka yi bayan ayyana birnin Kudus a matsayin babban birnin Isra’ilan.

Akalla Falasdinawa dubu 6 Isra'ilan ta hallaka tsakanin watan Maris zuwa Disamban bara
Akalla Falasdinawa dubu 6 Isra'ilan ta hallaka tsakanin watan Maris zuwa Disamban bara REUTERS/Ibraheem Abu Mustafa
Talla

Cikin sanarwar da kwamiti na musamman mai bincike kan rikicin yankin Gaza bayan zangar-zangar bara, ya fitar ya nuna yadda Isra’ila ta yi amfani da karfi kan masu zanga-zangar tsakanin ranakun 30 ga watan Maris har zuwa 31 Disamban 2018, tare da hallaka mutanen da basu jiba, basu gani ba.

Sanarwar wadda shugaban kwamitin Majalisar Dinkin Duniyar, Santiago Canton ya sanyawa hannu, ta ce Sojin Isra’ilan sun karya dokokin kare hakkin bil’adama ta yadda kwararru wajen iya harbi daga Isra’ilan suka hallaka fiye da Falasdinawa dubu 6, masu zanga-zanga ciki har da kananan yara da kuma jami’an lafiyar da ke aikin kai dauki baya ga ‘yan jarida.

Kwamitin wanda hukumar kare hakkin bil’adama ta Majalisar Dinkin Duniya ta kafa tun cikin watan Mayun bara, ya ce akwai kwararan hujjoji a hannunsa kan yadda Sojin Isra’ilan suka yiwa Falasdinawa masu zanga-zanga kisan kiyashi tun bayan fara boren, adawa da matakin ayyana birnin Kudus a matsayin babban birnin Isra’ilan da Amurka ta yi.

Sai dai tuni Isra’ilan ta bakin Firaministanta Benjamin Netanyahu ta musanta batun na Majalisar Dinkin Duniya, wanda ta kira da kage kana bin da bai faru ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.