Isa ga babban shafi
Duniya

Majalisar Dinkin Duniya tayi asarar ma’aikatan ta 72 a 2019

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres yace Majalisar tayi asarar ma’aikatan ta 72 a cikin wannan shekara, wadanda suka hada da fararen hula da kuma dakarun samar da zaman lafiya.

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guterres tareda wasu daga cikin ma'aikatan MDD
Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guterres tareda wasu daga cikin ma'aikatan MDD REUTERS/Djaffar Sabiti
Talla

Yayin da yake aje firanni domin bikin ranar ma’aikatan da ake kowacce shekara, Guterres yace daga cikin adadin wadanda suka mutu, 25 fararen hula ne, yayin da 43 kuma dakarun samar da zaman lafiya, sai kuma yan Sanda guda 4.

Sakataren yace ma’aikatan suna aiki a wurare masu hadari a Duniya, saboda haka ya zama wajibi a dinga yaba musu, yayin da ya mika sakon ta’aziya ga iyalai da yan uwan wadanda suka mutu.

Daga cikin yankunan da Majalisar Dinkin Duniya ta aike da janmi’an ta sun hada da Afrika irinsu Mali,DRCongo, Afgahanistan, Syria, Libya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.