Isa ga babban shafi
Amurka-Turkiya

Amurka ta bai wa Turkiya damar kai hari a Syria

Majalisar Dinkin Duniya ta ce, a shirye take ta tunkari duk wani mummunan al’amari a yankin arewa maso gabashin Syria bayan Amurka ta sanar da aniyarta ta janyewa domin bai wa sojojin Turkiya damar kaddamar da hare-hare kan mayakan Kurdawa. Tuni Kungiyar Tarayyar Turai ta gargadi cewa, farmakin na Turkiya zai cutar da fararen hula tare da rabba dimbin jama’a da muhallansu.

Wasu daga cikin dakarun Turkiya akan iyakar Syria
Wasu daga cikin dakarun Turkiya akan iyakar Syria (AFP)
Talla

Babban Jami’in Majalisar Dinkin Duniya da ke kula da ayyukan jin kai a Syria, Panos Moumtzis ya ce, ba su da masaniya kan abin da zai faru nan gaba, amma sun shirya tunkarar duk wani kazamin al’amari.

Turkiya ta yi barazanar kai hare-hare kan mayakan Kurdawa da take kallo a matsayin ‘yan ta’adda a Syria duk da cewa sun taka rawa wajen fatattakar kungiyar ISIS, yayin da Majalisar Dinkin Duniya ta ce, tana kan ganawa da bangarori da dama a yanzu haka.

Kodayake kawo yanzu Majalisar Dinkin Duniyar ba ta gargadi Amurka kai-tsaye ba biyo bayan matakin da ta dauka na bayar da damar kai hare-haren.

Majalisar na dari-darin samun sabbin alkaluman mutanen da ka iya rasa matsugunansu a dalilin farmakin, ko kuma a dakile hanyar bayar da kayayyakin agaji, ko kuma takaita zirga-zirgar jama’a a Syriar.

A halin yanzu dai, Majalisar ta Dinkin Duniya na bai wa kimanin mutane dubu 700 agajin gaggawa a yankin arewa maso gabashin Syriar.

Shugaban Turkiya, Recep Tayyip Erdogan ya ce, da yiwuwar nan kusa su fara kai farmakin cikin dare ba tare da wani gargadi ba, kuma tuni kasar ta kara karfin dakarunta akan iyakarta da Syria.

A gefe guda, kasar Turkiya ta ce, ba za ta zura ido ba har kungiyar ISIS ta sake bullowa ta kowacce hanya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.