Isa ga babban shafi
Turkiya-Syria

Amurka ta aike da tawagar ganawa da Erdogan kan Kurdawa

Wani lokaci a yau Alhamis mataimakin shugaban Amurka Mike Pence da sakataren harkokin wajen kasar Mike Pompeo, za su isa birnin Ankara don ganawa da Racep Tayyib Erdogan a yunkurin kawo karshen farmakin da Turkiyya ta kaddamar a arewacin Syria kan mayakan Kurdawa.

Shugaban Turkiya Recep Tayyib Erdogan tare da magoya bayansa a birnin Anakara. 16/10/2019.
Shugaban Turkiya Recep Tayyib Erdogan tare da magoya bayansa a birnin Anakara. 16/10/2019. Murat Cetinmuhurdar/Presidential Press Office/via REUTERS
Talla

Sai dai gabanin wannan ziyara, shugaba Donald Trump ya ce abu ne mai yiwuwa Kurdawan PKK da Turkiyya ke yaka sun fi mayakan IS ta’addanci.

Trump wanda ke gabatar da taron manema labarai, ya ce kungiyar 'PKK', wadda wani bangare na Kurdawa ne da ya share tsawon shekaru yana yakar Turkiya, ga alama ayyukan ta’addancinsa sun fi na IS muni ta kowace fuska.

Shugaba Recep Erdogan ya ce yana jiran isowar mataimakin shugaban na Amurka Mike Pence a birnin Ankara, sai dai ya yi kashedin cewa sam ba ya da niyyar dakatar farmakin da yake kai wa Kurdawan a cikin Syria har sai ya cimma maradunsa.

To sai dai shugaban mayakan Kurdawan da suka share tsawon sherkaru suna kawance da Amurka domin yaki da mayakan IS Mazloum Abdi, ya ce daga yanzu sun daina wannan yaki da mayakan IS, matakin da ke matsayin martani dangane da yadda Amurka ta juya masu baya.

Shi ma dai Kwamitin Tsaron Majalisar Dinkin Duniya wanda ya gudanar da zama na musamman a jiya laraba, ya yi gargadin cewa farmakin na dakarun Turkiya zai bai wa daruruwan ‘yan ta’adda da Kurdawan ke tsare da su a Syria damar arcewa daga gidajen jiya yari.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.