Isa ga babban shafi
China

Annobar Corona: Mutane kusan 400 sun halaka dubu, 17 sun kamu

Jami’an lafiya a China sun ce adadin mutanen da annobar murar mashako ta corona ta halaka a kasar ya kai kusan 400.

Wasu daga cikin daruruwan jama'ar dake kokarin sayen tsummokaran rufe hanci a birnin Manila na Philippines bayan bullar annobar murar corona acikin kasar daga China.
Wasu daga cikin daruruwan jama'ar dake kokarin sayen tsummokaran rufe hanci a birnin Manila na Philippines bayan bullar annobar murar corona acikin kasar daga China. AFP/Ted ALJIBE
Talla

Karuwar adadin na zuwa ne sa’o’i bayan da Philippines ta zama kasa ta farko da ta bada rahoton salwantar rai a dalilin wannan annoba, bayan bazuwar ta zuwa kasashe 24.

Da safiyar wannan litinin ce dai Ma’aikatar lafiyar kasar ta China, ta tabbatar da karuwar adadin wadanda annobar murar ta corona ta halaka daga 304 a ranar lahadi zuwa 361, yayinda kuma adadin wadanda suka kamu da cutar ya karu zuwa dubu 17da 205, bayan da annobar ta harbi wasu karin mutane dubu 2 da 829 a ranar lahadi kadai.

Yanzu haka dai kasashe na ci gaba da daukar matakin dakatar da zirga-zirgar jiragen sama tsakaninsu da China saboda annobar murar ta corona, yayinda Mongolia, Rasha da kuma Nepal suka rufe iyakokinsu na kasa da China.

A Thailand kuwa inda annobar murar coronar ta shafi mutane 19, likitoci sun bayyana warkewar wani mutum dan kasar China awanni 48 bayan karbar magani.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.