An zakulo gawarwakin mutanen da laka ta binne a Norway
Masu aikin agaji sun zakulo gawar mutun na biyar da zabtarewar laka ta binne a wani kauye da ke kusa da babban birnin Norway kamar yadda jami’an ‘yan sanda suka sanar a yau Lahadi, yayin da ake ci gaba da neman karin mutane biyar da suka bace.
Wallafawa ranar:
Ibtila’in ya auku ne a sanyin safiyar ranar Larabar da ta gabata, inda gidaje suka lalace har ma suka gusa daga ainihin mazauninsu a sanadiyar zabtarewar lakar a kauyen Ask mai tazarar kilomita 25 daga arewa maso gabashin babban birnin Oslo.
Tuni aka kwashe kimanin mutane dubu daya daga wannan kauye mai yawan al’umma dubu 5 domin sauya musu matsuguni saboda fargabar abin da ka iya aukuwa nan gaba, ganin cewa har yanzu ana jin alamar motsawar kasa a garin.
Jami’an agajin na amfani da karnuka da jiragen sama masu saukar ungulu wajen neman sauran mutanen da lakar ta binne.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu