Isa ga babban shafi
INDIA-ADDINI

Shugaban addinin da ya mallaki mata 39 ya mutu a India

Wani shugaban addini a kasar India da ya mallaki mata 39 da yara da jikoki akalla 127 ya mutu yana da shekaru 76 a duniya.

Firaministan India Narendra Modi a Ahmedabad ranar 12 Maris ta shekarar 2021
Firaministan India Narendra Modi a Ahmedabad ranar 12 Maris ta shekarar 2021 REUTERS - AMIT DAVE
Talla

Mutumin mai suna Zionnghaka Chana da yayi rayuwar sa a Jihar Mizoram a matsayin daya daga cikin shugabannin iyalan da suka fi yawa a duniya ya rasu ne sakamakon cutar suga da hawan jini a wani asibiti.

Babban Ministan Mizoram Zoramthanga ya bayyana cewar Jihar tasu tayi bankwana da Chana cikin matukar bakin ciki da kuma juyayi.

Ministan yace Mizoram da kauyen su na Baktawng Tlangnuam ya zama daya daga cikin wuraren da baki yan yawon bude ido ke tururuwa domin ganin iyalan sa.

Addinin mutanen garin da kakan Chana ya samar a shekarar 1930 na da mabiya akalla 1,700 da suka hada da iyalan gidan wadanda da dama daga cikin su suke sassaka katako da gina tukwane.

Manufar addinin Chana da ya dauko assali daga addinin Kirista ya nuna cewar akasarin limaman Kiristan sun ki amincewa da matsayin sa na auran mace fiye da guda.

Kafofin yada labaran Yankin sun ce Chana ya fara aure ne tun yana da shekaru 17.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.