An soke dokar da ta hana bude shaguna a lokutan Sallolin jam'i a Saudiya
Saudiyya ta amince a hukumance shaguna su ci gaba da kasancewa a bude a lokutan salloli 5 na Musulmai, a wani sauyi mai sarkakiya da kasar ke yi don tsamo kanta daga matsalar tattalin arziki.
Wallafawa ranar:
Tun da ya zama Yarima mai jiran gado na kasar a shekarar 2017, Mohammed bin Salman ya gabatar da sauye sauye na tattalin arziki da zamantakewa da ya tsara da zummar rage yawan dogaro da danyen mai da kasar ke yi.
A wata sanarwa, hukumar cinikayya ta Saudiyya ta ce z a ci gaba da harkokin tattalin arziki a gaba daya ranakun aiki, musamman a lokutan salloli na kowace rana.
Wannan sabuwar dokar ta cire da duk wani shamaki a game da kasuwanci da cinikayya , wanda hkumomin kasar suka ce yana janyo wa tatalin arziki asarar biliyoyin Riyals.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu