Saudiya
Saudiya ta jingine huldar zirga-zirga na jirage da kasashe uku
Ma'aikatar cikin gidan Saudiya ta bayyana dakatar da duk wata zirga-zirga ta jiragen sama tsakanin kasar da wasu kasashe uku da suka hada da Daular Larabawa, Habasha da kuma Vietnam.
Wallafawa ranar:
Talla
Cikin sanarwar da ta fitar, gwamnatin Saudiyan ta ce matakin da ya shafi kasashen 3 ya soma aiki ne daga yau Lahadi.
Saudiya ta ce matakin zai taimaka wajen takaita yaduwar cutar Covid-19 a cikin kasar.
A hukumance Saudiya ta gano mutane dubu 490 da suka harbu da annobar Korona, daga cikinsu kuma dubu 7 da 850 suka mutu.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu