Haiti
An gudanar da jana'izar shugaban kasar Haiti aka kashe cikin fargaba
A ranar Jumma’a Haiti ta gudanar da bikin bankwana ga tsohon shugaban kasar Jovenel Moise da aka kashe karkashin tsauraran matakan tsaro.
Wallafawa ranar:
Talla
To sai dai an ji karar harbe-harbe a wajen farfajiyar taron jana'izar, lamarin da ke tabbatar zaman dar-dar da kasar mai fama da talauci a yankin Caribbean ta shiga.
Fiye da makonni biyu bayan da aka kashe Moise mai shekaru 53 a gidansa da ke Port-au-Prince, wato safiyar ranar 7 ga watan Yulin, sai a jiya aka binne gawarsa babbar birnin yankin sa na Cap-Haitien, dake arewacin kasar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu