Isa ga babban shafi

Canada ta soma kwashe mutane daga Afghanistan

Gwamnatin Canada ta sanar da shirin ta na karbar yan gudun hijira daga Afghanistan  dubu 20 a wani tsari da gwamnatin kasar ta shifuda ganin matsakaicin yanayi da mutan kasar suka fada.

Babbam birnin Kabul na kasar Afghanistan
Babbam birnin Kabul na kasar Afghanistan REUTERS - OMAR SOBHANI
Talla

Ministan shige da fice na Canada ya bayyana cewa babu ta yada Canada za ta rufe idanu gani matsallolin da jama’a suka fada a kasar ta Afghanistan.

Birnin Kunduz bayan ya fada hannun yan Taliban
Birnin Kunduz bayan ya fada hannun yan Taliban AP - Abdullah Sahil

Jirgin farko dauke da yan kasar ta Afghanistan ya sauka filin tashi da saukar jirage na birnin Toronto na kasar ta Canada dauke da wasu daga cikin tsofin ma’aikata yan kasar Afghanistan da suka yi aiki da Canada a baya.

Shugaban Afghanistan Ashraf Ghani yan lokuta da isowar sa filin tashi da sauka na Mazar-i-Sharif
Shugaban Afghanistan Ashraf Ghani yan lokuta da isowar sa filin tashi da sauka na Mazar-i-Sharif AFP - -

Fadar Firaministan kasar ta Canada ta ce ta na bi sau da kafa yada lamura ke tafiya a kasar ta Afghanistan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.