Isa ga babban shafi
RIKICIN-AFGHANISTAN

Ya dace duniya ta hada kai domin tinkarar Afghanistan - Guterres

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya bukaci kasashen duniya da su hada kan su wajen murkushe barazanar ayyukan ta’addancin dake tasowa daga Afghanistan sakamakon karbe ikon da kungiyar Taliban tayi a kasar.

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres
Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres Javier Soriano AFP/Archivos
Talla

Yayin da yake tsokaci a taron gaggawa na kwamitin sulhu, Guterres yace ya zama wajibi duniya ta hada kai wajen hana Afghanistan zama dandalin aikata laifuffuka da kuma baiwa ‘Yan ta’adda mafaka.

Sakataren ya roki kwamitin sulhu da kasashen duniya gaba daya da suka hada kai wajen aiki tare wajen dakushe barazanar tsaron dake fitowa daga Afghanistan da kuma tabbatar da mutunta ‘yancin Bil Adama a cikin kasar.

Yadda Yan Taliban ke shawagi a birnin Kabul
Yadda Yan Taliban ke shawagi a birnin Kabul - AFP

Jawabin Guterres na zuwa ne bayan da mayakan Taliban ke ci gaba da shawagi a titunan birnin Kabul sakamakon nasarar da suka samu na karbe iko da kasar bayan shekaru 20.

Rahotanni sun ce dubban mutane ne suka mamaye tashar jiragen saman birnin Kabul inda manyan kasashen duniya suka aike da jirage domin kwashe ‘yan kasashen su domin barin kasar.

Sakatare Janar din yace kwanaki masu zuwa nan gaba na da matukar tasiri dangane da makomar kasar, yayin da kasashen duniya zasu zuba ido domin ganin abinda zai faru a kasar, inda yake cewa mutanen Afghanistan na bukatar taimako, kuma bai dace a juya musu baya ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.