Isa ga babban shafi
Haiti

Masu shigar da kara na tuhumar Firaministan Haiti da kisan shugaba Moise

Babban mai shigar da kara na Haiti ya mika bukatar fara tuhumar Firaministan kasar Ariel Henry dangane da kisan gillar da aka yiwa tsohon shugaban kasar Jovenel Moise.

Firaministan Haiti Ariel Henry.
Firaministan Haiti Ariel Henry. AP - Joseph Odelyn
Talla

Hujjoji na ci gaba da karfafa wadanda ke zargin hannun Firaministan a kisan shugaba Jovenel Moise yayin wani farmaki da mahara suka kai gidansa watanni kusan 3 da suka gabata.

Cikin wata wasika wadda ke matsayin ta 2 da sashen shigar da karar ya gabatarwa gwamnati ya nemi hukumar shige da fice ta kasar ta haramtawa Firaminista Ariel Henry barin kasar a kowanne yanayi.

Wata shaidar baya-bayan nan ta nuna yadda Henry ya yi waya da babban wanda ake zargi da kisan shugaban na Haiti, lokaci kankani bayan farmakin da ya hallaka shugaban.

Wasikar mai dauke da sa hannun babban mai shigar da kara ta kasar ta kuma nemi izinin gurfanar da Firaministan don amsa tuhuma dangane da alakarsa da maharan na ranar 6 ga watan Yuli.

Tun a juma’ar da ta gabata babban mai shigar da karar ya aikewa da Firaministan bukatar ganin ya bayyana gaban kotu jiya talata don amsa tambayoyi da ke matsayin kari kan bayyanarsa gaban mahukuntan kasar sa’o’I kalilan bayan kisan shugaba Moise amma kuma yaki mutunta gayyatar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.