Isa ga babban shafi
Coronavirus

Rigakafin corona na kwaya da Pfizer ya samar na da tasirin kashi 89

Kamfanin Pfizer ya yi ikirarin cewa sabon nau'in rigakafin Covid-19 na kwaya da ya samar na da tasirin yakar cutar da akalla kashi 89. Acewar kamfanin ikirarin nasa ya biyo bayan jerangiyar bincike da kuma gwaje-gwajen da ya aiwatar kan kwayar rigakafin.

Nau'in kwayar rigakafin corona da Pfizer.
Nau'in kwayar rigakafin corona da Pfizer. REUTERS - DADO RUVIC
Talla

Sanarwar da kamfanin na Pfrizer ya fitar ya ce yabi tsarin gwaje-gwaje ne bisa tanadin hukumomin lafiya na kasa da kasa gabanin tabbatar da sahihihancin maganin dama tasirin da ya ke da shi na yaka ko kuma kashe cutar baki daya da kashi 89.

Kamfanin na Pfizer da hadin gwiwar BioNTech na matsayin kan gaba a jerin kamfanonin magunguna 8 da suka samar da rigakafin cutar ta covid-19 wadda zuwa yanzu ta kashe mutane fiye da miliyan 5 a sassan duniya, ya zama kamfani na biyu bayan Merck na Amurka da ya yi ikirarin samar da rigakafin na kwaya.

Acewar kamfanin na Pfizer nau'in rigakafin nasa na kwaya mai suna Paxlovid zai taimake gaya wajen magance cutar, hana kamuwa da ita dama rigakafinta.

Kamfanin wanda ya bayyana samar da nau'in kwayar rigakafin a matsayin babbar nasara ga duniya baki daya la'akari da yadda cutat ke ci gaba da kisa ya yi ikirarin cewa nau'in kwayar zai taimaka wajen rage cunkoson da asibitoci ke gani a kokarin karbar allurar rigakafin.

Acewar kamfanin yanzu haka yana shirin mikawa hukumar kula da abinci da magunguna ta Duniya nau'in kwayar don kammala bincike tare da sahale fara amfani da shi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.