Isa ga babban shafi
RIKICIN-FARANSA-ALGERIYA

Faransa zata gabatar da bayanan asiri akan yakin Algeria

Kasar Faransa tace zata baiwa jama’a damar ganin bayanan asiri da ‘Yan Sandan kasar suka tattara dangane da yakin neman ‘yancin Algeria shekaru 15 kafin wa’adin da aka shirya gabatar da shi ga jama’a.

Shugaban Faransa Emmanuel Macron
Shugaban Faransa Emmanuel Macron Ludovic MARIN POOL/AFP
Talla

Gwamnatin Faransa tace takardun bayanan sun kunshi binciken da aka gudanar tsakanin 1954 zuwa 1962 lokacin da ‘Yan kasar Algeria suka gwabza fadar neman ‘yanci da sojojin ta, abinda ake ganin zai nuna yadda dakarun Faransa suka azabtar tare da kashe mutanen kasar.

Ministar al’adun Faransa Roselyne Bachelot tace suna da damar gina dangantakar su da Algeriya, amma za suyi nasarar haka ne kawai ta bin tafarkin gaskiya, sabanin rufa rufa akan abinda ya faru.

Ministan harkokin wajen Algeria Ramtane Lamamra
Ministan harkokin wajen Algeria Ramtane Lamamra RYAD KRAMDI AFP/File

Wannan mataki na zuwa ne a daidai lokacin da Faransa ke kokarin farfado da dangantakar dake tsakanin kasashen biyu wadda tayi tsami sakamakon matsalolin diflomasiyar da aka samu a watannin da suka gabata, lokacin da shugaba Emmanuel Macron ya zargi shugabannin kasar da kokarin rubuta sabon tarihin da zai haifar da kyama ga jama’ar kasar.

A wannan mako ministan harkokin wajen Faransa Jean Yves Le Drian ya ziyarci Algeria da zummar inganta dangantakar kasashen biiyu inda ya gana da shugabannin ta.

Kasar Faransa ta yiwa Algeria mulkin mallaka, kafin yakin da aka gwabza wanda ya kai ga shugaba Charles de Gaulle baiwa kasar ‘yanci a shekarar 1962.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.