Isa ga babban shafi
Amurka

Shugaba Biden, zai nada mace bakar fata cikin alkalan kotun kolin kasar.

Shugaban Amurka Joe Biden zai rantsar da mace ta farko kuma bakar fata daga cikin alkalan kotun kolin kasar, kamar yadda fadar White house ta tabbatar.

Shugaban Amruka Joh Biden
Shugaban Amruka Joh Biden Nicholas Kamm AFP
Talla

Wannan na nufin Sandra Day O’Cannor zata zama mace ta farko a matsayin guda daga cikin alkalan kotun, inda zata maye gurbin Stephen Breyer wanda zai yi ritaya a watan Yuni mai zuwa.

Sai dai har ya zuwa yanzu ba’a bayyana tsare-tsaren ritayar ta mai shari’a Stephen Breyer a hukumance ba.

Kotun kolin Amurka dai kamar ta sauran kasashe itace mai yanke hukunci na karshe kan duk wani al’amari da ya isa gaban kotu.

Bisa tarihi dai Sandra itace bakar Fata ta uku, kuma mace ta farko da zata yi aiki a matsayin alkali a kotun, bayan mai shari’a Thurgood Marshall wanda ya yi aiki a tsakanin shekarun 1967 zuwa 1991 da kuma mai shari’a Clarence Thomas.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.