Isa ga babban shafi

Shugaban Isra'ila zai ziyarci wasu kasashen Larabawa

Shugaban  kasar Israila Isaac Herzog ya fara ziyarar sa ta farko a kasar Daular Larabawa tun bayan da kasashen biyu suka kulla huldar diflomasiya.

 Isaac Herzog, tare da mai dakin sa  Michal Herzog, 
 a lokacin da Mohammed ben Zayed ya tarbe su a  Abou Dhabi
Isaac Herzog, tare da mai dakin sa Michal Herzog, a lokacin da Mohammed ben Zayed ya tarbe su a Abou Dhabi AP - Amos Ben Gershom
Talla

Wannan ziyarar na zuwa ne bayan ta Firaminista Naftali Bennett a watan jiya, inda rahotanni suka ce bangarorin biyu sun tattauna batutuwa da dama ciki harda da shirin nukiliyar Iran.

Ganawar hukumomin Isra'ila da Daular Larabawa
Ganawar hukumomin Isra'ila da Daular Larabawa Rashed AL-MANSOORI WAM/AFP

Kamfanin dillancin labaran kasar yace shugaban ya gana da Yariman Abu Dhabi Sheikh Mohammed bin Zayed Al Nahyan a fadar shugaban kasa.Wannan ziyara na zuwa kasa da wata daya da Isra'ila ta gabatar da wani kunshin matakan karfafa gwiwa ga yankunan yammacin gabar kogin Jordan da ta mamaye, bayan da Ministan Tsaron Kasar Benny Gantz a lokacin ya karbi bakuncin shugaban Falasdinawa Mahmud Abbas a ziyararsa ta farko cikin shekaru da dama.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.