Isa ga babban shafi
Masar-Isra'ila

Ziyarar Bennet a Masar ta jaddada manufar Isra'ila kan alaka da Larabawa

Ziyarar Firaministan Isra’ila Naftali Bennett a Masar da kuma ganawarsa da shugaba Abdel Fattah al-Sisi cikin makon nan ya sake bayyanawa karara yadda kasar ta Yahudawa ke kokarin gyatta alakar da ke tsakaninta da takwarorinta kasashen Larabawa. Ziyarar dai ita ce irinta ta farko cikin fiye da shekaru 10 da wani shugaban Isra'ila ke kaiwa Kasar ta Masar.

Ganawar shugaba Abdel Fattah al-Sisi na masar da Firaministan Isra'ila Naftali Bennett.
Ganawar shugaba Abdel Fattah al-Sisi na masar da Firaministan Isra'ila Naftali Bennett. - EGYPTIAN PRESIDENCY/AFP
Talla

A watan Agustan bara ne Isra’ila ta fara maido da dangantaka tsakaninta da wasu kasashen Larabawa, kuma hakan ne ya yi sanadin dawowar zumunci tsakaninta da kasashen hadaddiyar Daular Larabawa, Bahrain, Sudan da kuma Morocco.

Kafin wannan lokaci, kasashen Masar da Jordan ne kawai ke huldar diflomasiyya da Isra’ila, lamarin da ya sa sanarwar da tsohon shugaban Amurka Donald Trump ya yi a ranar 13 ga watan Agusta a kan cimma yarjejeniyar kulla dagantaka da Hadaddiyar Daular Larabawa ya zo da mamaki.

Sakamakon haka ne  ma  ranar 30 ga watan Agusta, Hadaddiyar Daular Larabawar ta janye dokar bijire wa Isra’ila, ta kuma soke batun biza a tsakaninsu, inda a washe garin ranar jirgin fasinjan Isra’ila na farko ya tashi daga Tel Aviv zuwa Abu Dhabi.

A watan Disamba, Morocco ta kasance kasar Larabawa ta 4 da ta maido da dangantaka da Israila, hakan ne ma ya sa Amurka ta saka mata da amincewa da ikonta a kan Yankin yammacin Sahara.

Hadaddiyar Daular Larabawa ta aike da jakadanta Isra’ila, Mohamed Al Khaja, a watan Maris, ya mika takardar kama aiki ga shugaba Reuven Rivlin na Isra’ila.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.