Isa ga babban shafi

Jamus,Faransa, Italiya da Birtaniya,sun dage matakan su na Covid19

Hukumar lafiya ta duniya WHO ta ce yawancin kasashen Turai, cikin su har da Jamus, Faransa, Italiya da Biritaniya, sun dage matakan su na Covid19 ba tare da la’akari da abin da hakan kan iya haifarwa, al’amarin da a yanzu ya haifar da karin adadin wadanda ke kamuwa da wani sabon nau’in mai suna BA2.

Tambarin hukumar kiwon lafiya ta Duniya WHO
Tambarin hukumar kiwon lafiya ta Duniya WHO REUTERS - DENIS BALIBOUSE
Talla

Daraktan hukumar kiwon lafiya ta Duniya WHO  yankin Turai Hans Kluge yayin wani taron manema labarai da ya gabatar a Maldovia, ya ce akwai kyaukkyawan fata game da makomar Turai, amma matakan da gwamnatocin nahiyar suka dauka, shakka babu zai haifar da da mara ido.

Wasu daga cikin baki yan yawon bude ido
Wasu daga cikin baki yan yawon bude ido AP - Sakchai Lalit

WHO ta ce adadin masu kamuwa da cutar Covid19 na ci gaba da karuwa a kasashe 18 cikin 53 da ke yankin.

Ya ce babban dalilin da ya haifar da karuwar shine mai yiwuwa sabon nau’in BA2, wanda ke saurin yaduwa, amma kuma duk da haka be kai sauran nau’o’in hadari ba.

Dangane da bayanan WHO, adadin sabbin alkaluman cutar Korona a Turai ya ragu sosai bayan wani matakin kololuwa da aka kai a karshen watan Janairu.

A cikin kwanaki bakwai da suka gabata, an sami sabbin alkaluman sama da mutum miliyan 5.1 da kuma mutuwar mutane sama da 12,400 a yankin Turai.

Hakan ya kawo adadin wadanda suka kamu da cutar tun bayan barkewar ta zuwa kusan miliyan 194.4 sannan adadin wadanda suka mutu ya zarce miliyan 1.92.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.