Isa ga babban shafi

Tsohon Shugaban Honduras zai gurfana gaban kotu a Amurka

An tisa keyar tsohon shugaban kasar Honduras Juan Orlando Hernandez zuwa Amurka domin gurfana a gaban kotu bisa zarginsa da laifin safarar daruruwan ton na hodar iblis zuwa Amurka tare da karbar cin hanci na miliyoyin dalloli.

Tsohon Shugaban kasar Honduras a hannun yan Sandan kasar
Tsohon Shugaban kasar Honduras a hannun yan Sandan kasar AP - Elmer Martinez
Talla

Juan Orlando Hernandez mai shekaru 53, wanda ya fuskanci zargen-zargen cin hanci da rashawa a wa'adin shugabancinsa tsakanin shekara 2014 zuwa 2022, idan har aka same shi da laifi yayin da yake gurfana yau jumma gaban wata kotu a birnin New York, to zai iya shafe sauran rayuwarsa a gidan yari.

Amurka da jimawa ta kaddamar da bincike biyo bayan zargin tsohon Shugaban kasar Honduras Juan Orlando Hernandez da hada-hada dama safarar hodar ibilis daga kasar sa zuwa Amurka.

Tsohon Shugaban Honduras Honduras Juan Orlando
Tsohon Shugaban Honduras Honduras Juan Orlando REUTERS - JORGE CABRERA

Ana zargin da fataucin kusan tan 100 na hodar ibilis,tarihi ya nuna ta yada wannan kotu ta yankewa wani dan uwansa hukunci bayan samun sa da fatauci hodar ibilis.

Wasu na dangata kama tsohon Shugaban kasar da bita da kulli daga abokanin hamaya a fagen siyasa,yayinda hukumar tsaron Amurka ta sheilatan cewa akwai sheidu a hannun hukumar bincike da kuma za a gabatar da su a yau juma'a.

Alkalan Juan Orlando Hernandez na fatan ganin an basu damar kare shi kamar dai yada doka ta bukaci a yi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.