Zaben Shugaban majalisar Honduras ya raba kawunan yan siyasar kasar
Yan Majalisun kasar Honduras suka baiwa hamuta iska a dai-dai lokacin zaben Shugaban majalisar dokokkin kasar a jiya juma’a.
Wallafawa ranar:
Rahotanni daga zauren majalisar na nuni cewa yan majalisu 20 daga cikin ya’an jam’iar sabuwar Shugabar kasar Xiomara Castro ne suka haifar da yammuci tareda neman ganin an zabi daya daga cikin su wato Jorge Calix a mammaikon mutumen da jam’iyyar ta tsayar da shi,wanda hakan ya sabawa yarjejeniyar da jam’iyyun suka cimma a baya.
Ministan cikin gidan kasar Leonel Ayala ya sheidawa manema labarai cewa dan majalisa Calix na samun goyan bayan yan majalisu 83 yayinda dokokkin hukumar ke ayana cewa duk mai neman kujear shugabancin majalisar ya zama wajibi ya samu goyan bayan yan majalisu 65 daga yan majalisu 128 da ake da su.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu