Isa ga babban shafi

Amurka ta yi tir da hukuncin kotun Arizona da ya haramta zubar da ciki

Fadar shugaban Amurka ta yi Allah wadai da hukuncin kotun Jihar Arizona wanda ya haramta zubar da ciki, wanda aka bayyana shi a matsayin abinda gwamnati ba za ta amince da shi ba.

Masu zanga-zangar bukatar halasta dokar zubar da ciki.
Masu zanga-zangar bukatar halasta dokar zubar da ciki. AP - J. Scott Applewhite
Talla

Mai Magana da yawun fadar shugaban, Karine Jean-Pirre ta ce muddin aka amince da wannan hukunci, ma’aikatan lafiiyar da suka taimakawa mata zubar da ciki, za su fuskanci daurin shekaru 5 a gidan yari.

Jean-Pirre ta ce wannan hukuncin zai tilastawa matan da aka yiwa fyade, ko kuma wadanda iyayensu suka yi wa ciki, goya cikin da kuma haihuwar sa, yayin da babu abinda matan da ke fuskantar hadari za suyi wajen ceto rayukansu.

Gwamnatin Joe Biden lokacin yakin neman zabe, ta bayyana aniyarta na halarta zubar da ciki ga matan da su ke bukatar yin haka saboda wasu dalilai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.