Isa ga babban shafi

Kasashen Turai na duba yuwuwar karfafa dangankata da yankin Balkan

Tarayyar Turai da shugabannin kasashen yankin Balkan suna cikin wani taro Talatar nan a birnin Tirana na Albania, don tattauna batun karfafa zumunci, a yayin da mamayar da Rasha ke yi a Ukraine ta farfado da kokarin kungiyar neman fadadawa.

Shugaban Serbia Aleksandar Vucic lokacin da yake gabatar da jawabi a wani babban taron yankin Balkan
Shugaban Serbia Aleksandar Vucic lokacin da yake gabatar da jawabi a wani babban taron yankin Balkan REUTERS - FLORION GOGA
Talla

Kasashen na yankin Balkan da suka shafe shekaru  suna jiran Tarayyar Turai ta karbe su sun bayyana takaicinsu a kan yadda har yanzu ake kan abu guda, musamman ma yadda tuni aka bai wa Ukraine da Maldova damar neman shiga kungiyar ta yammacin Turai.

Taron, wanda ya kunshi kasashen Albania, Bosnia, Montenegro, Kosovo, Arewacin Macedonia da Serbia, zai mayar da hankali ne a kan yaukaka hadin kai.

Yakin Ukraine ya dada jaddada wa Tarayyar Turai  mahimmancin kara azama wajen samar da kwanciyar hankali a yakin na Balkan, don dakile rinjayen Rasha da China, wadda ta zuba makudan kudade a bangaren samar da kayayyakin more rayuwa a kasar.

Daya daga cikin mahimman batutuwan dubawa a wannan taro  zai kasance tantance matakin sabuwar dangantaka  tsakanin Tarayar Turai da yankin Balkan, kamar yada bayanai sukaa nuna gabnin taron.

A watan Yuli, Tarayar Turaai ta bude tattaunawa a kan bukatar da  Arewacin Macedonia da Albania suka mikan a shiga kungiyar a shekarun baya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.