Isa ga babban shafi

Za mu hukunta kasashen da suka bijire wa yaki da dumamar yanayi - MDD

Majalisar dinkin duniya ta amince da daukar wani mataki da zai fara hukunta kasashen da ke fitar da hayaki da sinadaran da ke gurbata muhalli ba kuma tare da daukar matakin da ya dace ba. 

Wasu yara maza kenan dauke da abin diban ruwa yayin da suke komawa bukkokin su, bayan sun je rijiya neman ruwa a kauyen Ntabasi mai fama da matsalar fari a Samburu da ke Gabashin Kenya, an dauki wannan hoto ranar 14 ga watan Oktoba, 2022.
Wasu yara maza kenan dauke da abin diban ruwa yayin da suke komawa bukkokin su, bayan sun je rijiya neman ruwa a kauyen Ntabasi mai fama da matsalar fari a Samburu da ke Gabashin Kenya, an dauki wannan hoto ranar 14 ga watan Oktoba, 2022. AP - Brian Inganga
Talla

 

A wata kuri’ar jin ra’ayi tsakanin kasashe mambobin majalisar mai cike da tarihi da aka kada a ranart Laraba, da tsibirin Vanuatu ya bada shawara, ta kuma tanadi damar gurfanar da kasar da aka samu da saba wannan doka, gaban kotun duniya musamman idan wannan kasa ta yi kunnen kashi wajen bada gudumowa a yaki da gurbatar muhalli. 

Da yake jawabi bayan kada kuri’ar, Firaministan Tsibirin na Vanatau Ishmael Kalsakau yace wannan wani al’amari ne mai matukar muhimmanci da kuma tarihi, idan aka yi duba da yadda kasashe ke fadin batun yaki da dumamar yanayi amma basa hobbasa wajen dakatar da shi. 

Kafin fara daukar matakin gurfanar da kasashe masu kunnen kashi a gaban kotun duniyar, za’a fara fitar da tsare-tsaren hukunce-hukunce da za’a yanke matukar aka sami kasa da aikata wannan laifi. 

Ko da jagorancin majalisar dinkin duniya ke mayar da martani kan zargin dalilin da zai hana baiwa kananan kotuna damar yin wannan hukunci, sai ya ce wannan matsala ce da in har ba’a dauki matakin da ya dace cikin gaggawa ba, tabbas bala’o’in da ke da nasaba da sauyin yanayi zasu mamaye duniya. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.