Jam'iyyar Narendra Modi ta rasa kujerar jihar Karnataka
Sakamako daga hukumar zaben kasar Indiya na tabbatar da cewa jam'iyya mai mulki ta Firaminista Narendra Modi ta rasa kujerar ta a babbar jihar Karnataka ta kudancin kasar shekara guda kafin zaben kasa.
Wallafawa ranar:
Cikin farin ciki,an bayyana nasarar jam'iyyar adawa ta Congress Party,wanda hakan ke dada nuni cewa yan adawa na kokarin dawowa da karfi a siyasar Indiya duk da cewa ta na rike da wasu kejeru daban da sakamakon na yau.
Bharatiya Janata (BJP, mai kishin addinin Hindu) jam’iyyar Firaminista Modi ke rike da madafun iko na wannan yanki.
Jihar Karnataka tana da yawan jama'a sama da miliyan 60, kusan girman Biritaniya kuma babban birninta Bengaluru shine cibiyar fasahar Indiya.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu