Isa ga babban shafi

Za a shafe shekaru 5 a jere ana fama da tsananin zafi- Bincike

Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadin cewa tun daga shekarar da muke ciki ta 2023 zuwa 2027 zasu kasance masu tsananin zafi da ba a taba samu ba a tarihi, sakamakon yadda tiriri mai gurbata muhalli ke ci gaba da yawaita.

Fitar da tiriri mai gurbata muhalli na daga cikin dalilan da masana ke alakantawa da dumama Duniya.
Fitar da tiriri mai gurbata muhalli na daga cikin dalilan da masana ke alakantawa da dumama Duniya. © AFP PHOTO / EHT COLLABORATION / ESO / M. KORNMESSER
Talla

Kwararrun Majalisar kan yanayi sun bayyana cewa duniya za ta ga shekaru 5 a jere da za ayi tsananin zafi wanda ke da nasaba da dumamar yanayi da ke ci gaba da barazana ga halittun ban kasa.

Bayan wani taro da tawagar kwararrun ta gudanar, biyo bayan dogon bincike game da tsananin zafin da duniya ke gani, sun ce cikin shekaru 5 masu zuwa akwai hasashen yiwuwar a iya samun shekara guda marar tsananin zafi.

Kafin wannan bincike na kwararrun dai shekarar 2015 zuwa 2022 su ne ke matsayin shekaru mafiya tsananin zafi da duniya ta gani, yayinda zafin na wannan karon ke kokarin zarce wanda aka gani a wadancan shekaru.

A cewar kwararrun shekara bayan shekara tsananin zafin zai ci gaba da rubanya wa matukar ba a sauki matakan da suka kamata wajen rage fitar da tiriri mai guba da manyan kasashe masu masana’antu ke yi ba.

Yarjejeniyar yanayi ta birnin Paris a shekarar 2015 da kasashe da dama suka sanyawa hannu dai ta amince da rage tiririn da ake fitarwa zuwa akalla 1850 ko 1900 ta yadda yanayin ba zai haura maki 1.5 a ma’aunin yanayi na Celcius ba amma kuma kasashe suka gaza mutunta yarjejeniyar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.