Isa ga babban shafi

Harin Rasha a Arewacin Ukraine ya kashe mutum 7

An kashe mutane bakwai ciki har da wata yarinya ‘yar shekara 6, mutum 144 kuma suka jikkata, sannan 41 na kwance a asibiti bayan da wani makami mai linzami na Rasha ya afkawa tsakiyar birnin Chernihiv mai tarihi a arewacin Ukraine a ranar Asabar.

Masu aikin ceto da ke kokarin kai daukin gaggawa ga mutanen da harin Rasha ya rutsa da su a Chernihiv, ranar 19 ga watan Agustan 2023.
Masu aikin ceto da ke kokarin kai daukin gaggawa ga mutanen da harin Rasha ya rutsa da su a Chernihiv, ranar 19 ga watan Agustan 2023. via REUTERS - STATE EMERGENCY SERVICE OF UKRAI
Talla

Shugaban kasar Volodymyr Zelenskiy a cikin jawabinsa na faifan bidiyo, wanda ya gabatar da safiyar Lahadi a karshen ziyarar da ya kai kasar Sweden, ya tabbatar da cewa sojojin kasarsa za su ba da martani ga Rasha kan wannan harin ta'addanci.

Ya ce daga cikin mutane 144 da suka jikkata, 15 yara ne, ya kuma bayyana sunan yarinyar da Sofia.

Wasu 15 kuma da suka samu raunuka jami'an 'yan sanda ne, in ji ministan harkokin cikin gida Ihor Klymenko a tashar Telegram. Klymenko ya ce yawancin wadanda abin ya shafa suna cikin motoci ne, ko kuma suna tsallaka hanya, ko kuma suna dawowa daga coci.

Gwamnan yankin Viacheslav Chaus ya ce mutane 41 na kwance a asibiti yanzu haka.

Harin Chernihiv, wanda ya kasance wani birni mai majami'u da suka shafe shekaru aru-aru wanda ke da tazarar kilomita 145 daga arewacin Kyiv, ya zo daidai da ranar hutun mabiya darikar Orthodox.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.