Isa ga babban shafi

Amurka: Trump zai mika kansa a kama shi a Georgia

A wannan Alhamis ne tsohon shugaban Amurka, Donald Trump, zai mika wuya a gidan yarin Georgia, a wani mataki na shari'ar aikata laifuka karo na hudu da yake fuskanta, yayin da yake ci gaba da fafutukar sake karbe ikon fadar White House a zabe mai zuwa.

Trump ya yi watsi da tuhume-tuhume guda hudu da aka shigar a kansa a matsayin shirme kuma ya ce ana masa bita da kulli.
Trump ya yi watsi da tuhume-tuhume guda hudu da aka shigar a kansa a matsayin shirme kuma ya ce ana masa bita da kulli. AP - Mary Altaffer
Talla

Za a tsare tsohon shugaban mai shekaru 77 a gidan yari na Fulton County da ke Atlanta, inda ake zargin sa da hada baki da wasu mutane18 da ake tuhumar su da yunkurin sauya sakamakon zaben 2020.

Wannan matakin kan hamshakin attajirin, na zama na farko da ya taba fuskanta, abin da ke zuwa ne 'yan sa'o'i kadan bayan ya yi biris da wata muhawara ta farko da ta kunshi abokan hamayyarsa takwas da ke neman takarar shugaban kasa a jam'iyyar Republican a 2024.

Trump bai halarci dandalin muhawarar da aka yi a gidan talabijin a Milwaukee, Wisconsin ba.

Da aka tambaye su ko za su goyi bayan Trump a matsayin dan takarar jam’iyyar koda an same shi da laifi a daya daga cikin laifuka hudu da yake fuskanta, kowanne dan takara ya daga hannunsa, in ban da tsohon gwamnan Arkansas Asa Hutchinson da tsohon gwamnan New Jersey Chris Christie.

Trump ya yi watsi da tuhume-tuhume guda hudu da aka shigar a kansa a matsayin shirme kuma ya ce ana masa bita da kulli wajen amfani da ma'aikatar shari'a karkashin shugaban jam'iyyar Democrat Joe Biden don dakile yunkurinsa na sake komawa fadar White House.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.