Isa ga babban shafi

Rasha ta tabbatar da mutuwar Prigozhin a hatsarin jirgin sama

Mahukuntan Rasha sun ce shugaban Kamfanin Sojin Hayar Wagner, wanda ya yi yunkurin hambarar da shugabancin rundunar sojin Rasha a watan Yuni, Yevgeny Prigozhin yana cikin jirgin da ya yi hatsari a ranar Laraba, inda dukkanin fasinjojin cikinsa suka mutu. 

Gwamnatin Rasha ta tabbatar da mutuwar Yevgeny Prigozhin
Gwamnatin Rasha ta tabbatar da mutuwar Yevgeny Prigozhin AP
Talla

Faduwar wannan jirgi na zuwa ne watanni  biyu bayan da Yevgeny Prigozhin ya kaddamar da wani gajeren bore da aka bayyana a matsayin kalubale mafi girma da shugaba  Vladimir Putin ya taba fuskanta  tun da ya  dare  karagar mulkin Rasha. 

Tun daga wannan lokaci ne rashin tabbas ya dabaibaye makomar sojin hayar Wagner da shugabansa mai yawan haddasa cece-kuce. 

A Larabar nan ce Ma’aikatar  Kula da Ayyukan Daukin Gaggawa ta kasar ta sanar da faduwar wani jirgin sama tsakanin Moscow da Saint Petersburg, kuma dukkannin fasinjoji 10 na cikinsa sun mutu. 

Daga bisani, Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Sama ta Rasha ta ce shugaban Wagner yana cikin wannan jirgi samfurin Embraer – 135 tare da wani babban kwamandan kamfanin, Dmitry Utkin.

Masu aikin agaji na kwashe gawarwakin fasinjojin jirgin da ya yi hatsari a Rasha.
Masu aikin agaji na kwashe gawarwakin fasinjojin jirgin da ya yi hatsari a Rasha. AP

A martanin da ya mayar da jin wannan labari, shugaban Amurka Joe Biden ya ce bai yi mamaki ba ko kadan da mutuwar jagoran na sojin Wagner. 

An gano gawarwakin 8 daga cikin fasinjojin wannan jirgi ya zuwa yanzu a yayin da shugaban Rasha Vladimir Putin bai ce uffan ba a game da lamarin. 

Shugaba Putin ya bayyana Prigozhin a matsayin maciyin amanar kasa kafin daga bisani suka cimma wata yarjejeniya da ta tilasta masa yin gudun hijira zuwa Belarus.

A cikin wannan makon ne, wani faifen bidiyo ya nuna Prigozhin tsaye da zungureriyar bindiga a wani yanki na Sahel a nahiyar Afrika, a daidai lokacin da Wagner ta fara daukar sojoji daga nahiyar ta Afrika  a cewar rahotanni.

Tuni Kamfanin Sojin Hayar na Wagner ya yi zargin cewa, sojojin Rasha masu tsaron sararin samaniya ne suka kakkabo jirgin da Prigozhin ke ciki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.