Isa ga babban shafi

Shugaban Wagner ya isa Belarus don zaman hijira

Shugaban kamfanin sojin hayar  Wagner Yevgeny Prigozhin wanda ya tashi zuwa kasar Belarus a jirgin samansa ya sauka a kasar, inda ya samu mafaka, a daidai lokacin da Rasha ke ikirarin cewa mayakan rundunar sun amince su mika makamansu bayan boren da suka yi a karshen makon da ya gabata.

Shugaban kaamfaanin sojin hayar Wagner, Yevgeny Prigozhin.
Shugaban kaamfaanin sojin hayar Wagner, Yevgeny Prigozhin. via REUTERS - PRESS SERVICE OF "CONCORD\
Talla

Shugaban Belarus, Alexander Lukashenko, ne ya tabbatar da isar Prigozhin kasarsa ta kamfannin dillancin labaran kasar, Belta.

Shugaban Belarus wandaya taka gagarumarrawadominkawokarshentawayen na kamfanin Wagner,  yacelallealaka ta yitsamimatukatsakanin Vladimir Putin da YevgenyProgozhin, dominshi ne yaroki Putin kada  yakashejagorankamfaninna Wagner bayan da aka murkusheyunkurinsanaafkawabirnin Moscow. 

A ranar Asabar aka  yi wa Prigozhin, mai shekaru 62  ganin karshe  tun bayan da ya bar Rostov-on-Don, wani babban birni da ke kudancin Rasha, wanda dakarunsa suka mamaye na dan lokaci.

Prigozzhin, wanda ya taba zaman gidan yari a lokuta dabam dabam a zamanin rusashiyar Tarayyar Soviet, ya zama hamshakin attajiri, wanda ya mallaki kamfanin sojin haya mafi girma da nagarta a Rasha, kuma babban abokin shugaba Vlaadimir Putin ne kafin yanzu.

Tun da farko a ranar Talata, sai da hukumar tsaron Rasha ta FSB ta janyue dukkanini tuhume-tuhume da ake wa dakarun da ke da hannu a tawayen Wagner, a matsayin wani bangare na yarjejeniyar da shugaban Belarus da Putin suka cimma.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.