Isa ga babban shafi

An tsare Trump a gidan yari na dan gajeren lokaci

An tsare tsohon shugaban Amurka, Donald Trump na dan gajeren lokaci a gidan yarin jihar  Georgia a jiya Alhamis, bisa zargin yukurin hadin baki don murda sakamakon zaben tare da amfani da karfin mulkinsa ba bisa ka’ida  ba.

Hoton da jami'an gidan yarin Fulton suka dauka na tsohon shugaban Amurka Donald Trump, bayan ya mika kansa.
Hoton da jami'an gidan yarin Fulton suka dauka na tsohon shugaban Amurka Donald Trump, bayan ya mika kansa. © Bureau du sheriff du comté de Fulton / via Reuters
Talla

Daga bisani an bayar da belinsa a kan kudi dala dubu dari 2, bayan da aka dauki hoton fuskarsa, kamar yadda aka saba yi wa masu aikata laifi. 

Trump, wanda ake zargi da hadin baki da wasu mutane 18 don murda sakamakon zaben shugaban kasa na shekarar 2020 a jihar Georgia da ke kudancin kasar, ya shafe kasa da mintina 30 a gidan yarin Fulton County dake Atlanta, kafin daga bisani ya bar wurin a cikin ayarin motocinsa na kasaita zuwa filin tashi da saukar jiragen sama. 

Kamar dai sauran wadanda ake  zarginsu tare, wadanda su ma suka mika kansu, an dauki hoton fuskar Trump mai shekaru 77, a yayin da ake shigar da shi zuwa gidan yarin, karo na farko da aka taba yi wa wani shugaban Amurka, mai ci ko kuma tsoho. 

Da yake jawabi bayan da aka sake shi, Trump wanda yake kan gaba a cikin masu neman takarar shugabancin Amurka a jam’iyyar Republican, ya bayyana ranar a matsayin ranar  bakin ciki ga  Amurkawa, yana mai jaddada cewa bai aikata ba daidai ba. 

Wannan ne karo na 4 da ake tuhumar tsohon shugaban Amurkan, kuma hamshakin attajiri  a kan aikata laifi tun daga watan Afrilu abin da ke gare  shi a matsayin babban kalubale ga  kudirinsa na neman sake zama shugaban kasar a karo na biyu. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.