Isa ga babban shafi

Dole ne mu tallafawa kananan kasashe yaki da dumamar yanayi - Indiya

Firaministan Indiya, Narendra Modi, ya ce dole ne shugabannin da za su halarci taron G20 da yake jagoranta a karshen mako, su tallafa wa kasashe masu tasowa don tunkarar sauyin yanayi da karin kudade da kuma musayar fasahohin kimiyya.

Narendra Modi yayin gabatar da jawabi a taron kasuwanci na B20, gabanin taron kasashen G20 da za a gudanar a New Delhi.
Narendra Modi yayin gabatar da jawabi a taron kasuwanci na B20, gabanin taron kasashen G20 da za a gudanar a New Delhi. AP - Manish Swarup
Talla

Dangane da koma bayan yaki da dumamar yanayi da tsananin zafin rana a fadin duniya da ake fama da shi, masana kimiyyar yanayi da masu fafutuka sun yi gargadin illar da ke tattare da hakan, musamman ga kasashe masu tasowa, idan shugabanni suka kasa cimma matsaya.

Taron kasashen na G20, wanda za a gudanar a New Delhi a karshen wannan makon, ya kunshi kasashe 19 da wakilan kungiyar Tarayyar Turai, wadanda ke da kusan kashi 85 cikin 100 na ma’aunin GDP a duniya.

Kasashe masu karfin tattalin arziki sun yi watsi da alkawarin da suka yi na samar da, dala biliyan 100 a duk shekara nan da shekarar 2020, amma ga kasashe masu fama da talauci, wato kasashen da ke bada gudun mowa sosai wajen gurbata muhalli za su taimaka wa kasashe masu rauni da ba su da alhakin haifar da dumamar yanayi da ake fama da shi, don tunkarar kalubalen sauyin yanayi.

Taron ministocin makamashi na G20 da aka gudanar a watan Yuli ya kasa cimma matsaya kan yadda za a takaita amfani da man fetur ko kuma kwal, da kuma gurbataccen man da ya kasance babban tushen makamashi ga kasashe kamar Indiya da China.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.