Isa ga babban shafi
ZABEN AMURKA

Kotu ta wanke Trump don ba shi damar shiga takarar fidda gwani

Kotun kolin Michigan, ta ce ba za ta saurari karar da wasu mutane hudu a jihar suka shigar da ke neman hana tsohon shugaban kasar Amurka, Donald Trump, shiga zaben fidda gwani na jam'iyyar Republican a ranar 27 ga watan Fabrairu ba, saboda rawar da ya taka a harin da aka kai majalisar dokokin kasar a ranar 6 ga Janairun 2021.

Tsohon shugaban Amurka, Donald Trump kenan, lokacin da yake fita daga harabar kotu.
Tsohon shugaban Amurka, Donald Trump kenan, lokacin da yake fita daga harabar kotu. © Mike Segar / Reuters
Talla

 

Masu shigar da kara dai, sun yi zargin Trump, wanda ke kan gaba cikin jerin masu neman kujerar shugabancin kasa karkaashin jam'iyyar Republican a shekarar 2024, ba zai iya zama shugaban kasa ba a karkashin wani tanadi na kundin tsarin mulkin Amurka da ya haramta wa mutane rike mukamai idan aka same su dumu-dumu cikin masu tayar da hankali ga zaman lafiyar Amurka.

Trump a wani sako da ya wallafa a shafinsa na True Social ya ce kotun ta musanta abin da ya kira yunkurin da 'yan jam'iyyar Democrat suka yi na haramta masa kada kuri'a a Michigan.

Hukuncin na Michigan ya banbanta da hukuncin da babbar kotun Colorado ta yanke a makon da ya gabata na hana Trump, shiga cikin masu tsayawa takara, inda Trump ya sha alwashin daukaka kara kan hukuncin Colorado zuwa kotun kolin Amurka.

An tuhumi Trump da taka rawa wajen yunkurin juyin mulki a zaben 2020 amma ba a tuhume shi da laifin tayar da kayar baya ba, da ya shafi harin ranar 6 ga watan Janairu.

Hukuncin da kotun kolin Amurka ta yanke zai iya warware batun sarkakiyar da ke iya bayyana cancantar Trump ko a akasin haka a fadin kasar na tsayawa takara a zaben 2024.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.