Isa ga babban shafi

Wani mutum a Spain ya barar da giyar da kudinta ya kai yuro miliyan 2 da rabi

Duniya – Wani mutum da ba’a iya tantance ko waye ba a kasar Spain, ya kutsa kai wani kamfanin sarrafa barasa inda ya zubar da giyar da aka mata kudi a kan yuro miliyan biyu da rabi ko kuma dala miliyan 2 da dubu 700.

Wani ma'aikacin otel yana zuba giya
Wani ma'aikacin otel yana zuba giya REUTERS/Yves Herman/Files
Talla

Hotunan bidiyon da na’ura ta nada wanda kamfanin barasar da ake kira Cepa 21 ya gabatar, ya nuna yadda mutumin ya dinga bin bakin kan famfon injinan sarrafa barasar yana bude su suna zubar da giyar, matakin da aka ce ya yi sanadiyar zubewar akalla lita dubu 60 na giyar.

Kamfanin yace lamarin ya auku ne da misalin karfe 3.30 na asuba a ranar lahadin da ta gabata, kuma giyar da aka yi asara na iya kai wa kwalba dubu 80.

Shugaban kamfanin Jose Moro yace babu tantama daga hotunan da suka gani na mutumin lokacin da yake bude famfunan, ya tabbatar da cewar da niyya ya aikata domin sanya su suyi asara.

Moro yace abinda suka fahimta shine mutumin da ya aikata laifin maketaci ne wanda ke cike da mugunta a zuciyar sa, kuma nufin sa shine ya sa su asara, domin babu abinda aka dauka a cikin kamfanin.

Tuni kamfanin ya gabatar da kara a gaban ‘yan sanda domin gudanar da bincike a kai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.