Isa ga babban shafi

Marocco ta cafke wani jirgin ruwa dauke da bakin haure sama da 100

Dakarun da ke tsaron gabar ruwa a Morocco sun sanar da kama wani jirgin ruwa dauke da mutane 141, wanda ke kan hanyar sa ta shiga Spaniya, dai-dai lokacin da ake samun karuwar fitar bakin haure daga Afirka zuwa turai tun daga farkon shekarar nan.

Wasu 'yan ci rani yayin kokarin tsallaka ruwa don shiga tsibirin Cueta dake kasar Spain.
Wasu 'yan ci rani yayin kokarin tsallaka ruwa don shiga tsibirin Cueta dake kasar Spain. AP - Antonio Sempere
Talla

Dakarun masarautar ta Morocco sun ce sun kama jirgin ne cikin daren ranar Lahadi, kuma anyi sa’a babu wanda ya rasa ransa cikin mutanen da ke cikin jirgin.

Bayanai sun ce dukannin mutanen sun fito ne daga kasashen Yammacin Saharar Africa.

Wannan shine kame mafi girma da mahukuntan Morocco suka gudanar a wannan shekara.

Ta cikin wani bayani da ministan harkokin cikin gidan Spaniya ya yi a baya-bayan nan, ya ce daga ranar daya ga watan Janairu zuwa 15 ga watan da muke ciki na Fabrairu, bakin haure 11,704 ne suka isa tsibirin Canary na gabar kasar, ninki 6 na adadin da aka gani a bara a irin wannan lokaci.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.