'Yan ci rani 32,000 ne suka tsallaka tekun Atlantika zuwa Spain a bana
Sabbin alkaluman da ma’aikatar harkokin cikin gidan Spain ta fitar, sun nuna cewar ‘yan ci rani akalla dubu 32 ne suka samu nasarar shiga tsibirin Canary na kasar a wannan shekara kadai, bayan tsallaka tekun Atlantika.
Wallafawa ranar:
Bayanai sun ce akasarin ‘yan ci ranin sun fito ne daga Senegal, yayin da ragowar suka fito daga kasashen Gambia, Mauritania, Morocco da kuma yankin yammacin Sahara.
Dubban ‘yan ci rani daga kasashen Afirka dai sun shafe shekaru suna amfani da tsibirin Canary da ke karkashin Spain a matsayin zangon farko, kafin karasa tsallakawa cikin nahiyar Turai.
Mahukuntan Spain sun ce daga ranar 1 ga watan Janairu zuwa 5 ga watan Nuwamban da muke, ‘yan ci rani akalla dubu 32, da 29 ne suka tsallaka teku zuwa tsibirin na Canary, adadin da ya zarta wanda aka gani a shekarar 2006, lokacin da bakin-haure dubu 31, da 678 suka tsallaka zuwa yankin.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu