Isa ga babban shafi
Ranar Mata ta Duniya

Yadda aka gudanar da bikin Ranar Mata ta Duniya cikin hotuna

A yayin da ake bikin Ranar Mata ta Duniya a yau Juma'a, dimbin mata ne a sassan duniya suka fantsama kan tituna suna gudanar da zanga-zanga domin nuna adawa da irin cin zarafin da suke fuskanta da kuma yadda ake nuna musu wariya ta bangarori da dama na rayuwa.

Daruruwan matan Indonesia sun fantsama kan tituna a wannan rana ta mata a duniya, inda suke fafutukar tabbatar da tsarin dimokuraidyya yadda ya kamata a kasar.
Daruruwan matan Indonesia sun fantsama kan tituna a wannan rana ta mata a duniya, inda suke fafutukar tabbatar da tsarin dimokuraidyya yadda ya kamata a kasar. AP - Dita Alangkara
Talla
Dimbin jama'a sun halarci bikin tabbatar da 'yancin zubar da ciki a Faransa a yayin da ake gudanar da bikin Ranar Mata ta Duniya a yau Juma'a a birnin Paris.
Dimbin jama'a sun halarci bikin tabbatar da 'yancin zubar da ciki a Faransa a yayin da ake gudanar da bikin Ranar Mata ta Duniya a yau Juma'a a birnin Paris. © Gonzalo Fuentes / Reuters
Wata mata dauke da allon neman karfafa wa mata guiwa a yayin gudanar da bikin Rana ta Duniya a birnin Berlin na Jamus.
Wata mata dauke da allon neman karfafa wa mata guiwa a yayin gudanar da bikin Rana ta Duniya a birnin Berlin na Jamus. REUTERS - Annegret Hilse
Wani majigi dauke da tallar karfafa wa mata guiwa wanda aka nuna a birnin London a wannan Rana ta Mata a Duniya.
Wani majigi dauke da tallar karfafa wa mata guiwa wanda aka nuna a birnin London a wannan Rana ta Mata a Duniya. REUTERS - Hollie Adams
Wasu mata Jamusawa dauke da allon neman mara wa mata baya a Jamus a bikin Ranar Mata ta Duniya
Wasu mata Jamusawa dauke da allon neman mara wa mata baya a Jamus a bikin Ranar Mata ta Duniya REUTERS - Annegret Hilse
Matan Azerbaijan sun gudanar da zanga-zangar neman karfafa wa mata guiwa a wannan Rana ta Mata a Duniya a birnin Baku
Matan Azerbaijan sun gudanar da zanga-zangar neman karfafa wa mata guiwa a wannan Rana ta Mata a Duniya a birnin Baku REUTERS - Aziz Karimov
'Yan matan Montenegro kenan ke gudanar da bikin Ranar Mata ta Dunya cikin nishadi a Podgorica.
'Yan matan Montenegro kenan ke gudanar da bikin Ranar Mata ta Dunya cikin nishadi a Podgorica. REUTERS - Stevo Vasiljevic
Bayan tabbatar da 'yancin zubar da ciki a Kundin Tsarin Mulkin Faransa a yau Juma'a, wasu daga cikin 'yan mata sun yi hoto cikin murna da shugaban kasar Emmanuel Macron.
Bayan tabbatar da 'yancin zubar da ciki a Kundin Tsarin Mulkin Faransa a yau Juma'a, wasu daga cikin 'yan mata sun yi hoto cikin murna da shugaban kasar Emmanuel Macron. REUTERS - Gonzalo Fuentes
Wata matashiya kenan a Lebanon dauke da allo mai kunshe da sako kan irin mawuyacin halin da mata ke ciki a Zirin Gaza a yayin bikin Ranar Mata ta Duniya.
Wata matashiya kenan a Lebanon dauke da allo mai kunshe da sako kan irin mawuyacin halin da mata ke ciki a Zirin Gaza a yayin bikin Ranar Mata ta Duniya. REUTERS - Mohamed Azakir
'Yan matan Rome ba a bar su a baya ba wajen gudanar da zanga-zangar neman bai wa mata 'yancinsu a yayin bikin Ranar Mata ta Duniya.
'Yan matan Rome ba a bar su a baya ba wajen gudanar da zanga-zangar neman bai wa mata 'yancinsu a yayin bikin Ranar Mata ta Duniya. REUTERS - Yara Nardi
An gudanar da tattaki a Japan domin nuna wa duniya irin muhimmancin mata a wannan Rana ta Mata a Duniya
An gudanar da tattaki a Japan domin nuna wa duniya irin muhimmancin mata a wannan Rana ta Mata a Duniya REUTERS - Issei Kato

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.