Isa ga babban shafi

Mata miliyan 230 aka yi wa kaciya a duniya- UNICEF

Wani rahoto da Hukumar Kula da Kananan Tara ta Majalisar Dinkin Duniya UNICEF ta fitar ya bayyana cewa, sama da mata da suka hada da manya da kananan yara miliyan 230 ne aka yi wa kaciya, wadanda kuma akasarinsu na zaune ne a Afirka.

Wata 'yar kasar Baringo kenan da aka riketa zuwa inda za ta huta bayan an yi mata kaciya a shekarar 2014.
Wata 'yar kasar Baringo kenan da aka riketa zuwa inda za ta huta bayan an yi mata kaciya a shekarar 2014. REUTERS/Siegfried Modola
Talla

Rahoton wanda UNICEF ta fitar a jiya Juamma’a, ya ce cikin shekaru takwas da suka wuce, kimanin mutane miliyan 30 ne aka yi wa wannan aiki, kaciyar da ta ce ke haifar da matsaloli da dama ga mata da suka hada da yoyon fitsari da rikicewar al'ada.

Hukumar ta ce duk da cewa akwai raguwar yawan  mata da ake yi wa kaciyar, ta yi kira da a kara kaimi a kokarin da ake yi na kawar da wannan al'ada da ke ci gaba da yaduwa cikin al'ummomi da dama musamman a nahiyar Africa.

Somaliya ce ke kan gaba a jerin kasashen da aka fi yin kaciyar mata, inda kashi 99 cikin 100 na yawan mata masu shekaru 15 zuwa 49 an yi musu kaciya a kasar.

Alkaluman binciken ya kuma nuna acewa, Burkina Faso ta samu ci gaba a raguwar kason mata ‘yan tsakanin shekaru 15 zuwa 49 da ake yi wa wannan aiki aika-aika daga kashi 80% zuwa 30% cikin shekaru talatin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.