Isa ga babban shafi

Ba zan goyi bayan Donald Trump a zaben shugaban kasar Amurka - Mike Pence

Tsohon mataimakin shugaban kasar Amurka Mike Pence ya janye daga cikin masu goyan bayan Donald Trump a zaben shugaban kasar da za a yi a watan Nuwamba na wannan shekara ta 2024.Sanarwar ta haifar da rudani a jam’iyyar Republicain wanda ake ganin cewa zai yi wuya Donald Trump ya magance matsalar da jam’iyyar ke fama da ita.

Mike Pence Tsohon mataimakin Shugaban Amurka
Mike Pence Tsohon mataimakin Shugaban Amurka AP - John Locher
Talla

Mike Pence, mai shekaru 64, yayin wata hira da Fox News ya na mai cewa "Ba zai ba ku mamaki ba, ba zan goyi bayan Donald Trump ba a wannan shekara ba,Mike Pence dan jam'iyyar Republican ya zargi tsohon shugaban nasa da bayar da shawarar marar kyau wanda hakan ya sabawa ra'ayin mazan jiya.

Pence mai tsananin adawa da zubar da ciki, ya taimaki Donald Trump ya taka muhimiyar rawa a lokutan zabe na shekarar 2016 ya kasance da Donald Trump a yakin neman zaben shugaban kasa na shekarar.

Mike Pence tsohon mataimakin shugaban Amurka
Mike Pence tsohon mataimakin shugaban Amurka REUTERS - EDUARDO MUNOZ

ike Pence na ci gaba da nuna damuwa ganin ta yada wasu magoya bayan Donal Trump suka kai hari a majalisa da aka sani da Capitol, wanda ya girgiza demokradiyyar Amurka a ranar 6 ga Janairu, 2021.

A wannan rana, Mike Pence ya jagoranci, a matsayin mataimakin shugaban kasa, zaman da aka yi a majalisa, inda zababbun jami'ai suka tabbatar da nasarar Joe Biden a zaben shugaban kasa na 2020.

Yayin wannan arrangama ta majalisa,wasu daga cikin maharan sun bukaci a rataye Mike Pence, wanda tare da taimakon wasu jami’ai ya ɓoye cikin gaggawa.

Tsohon mataimakin Shugaban Amurka  Mike Pence da dan takara  Donald Trump
Tsohon mataimakin Shugaban Amurka Mike Pence da dan takara Donald Trump AP - Evan Vucci

Tun daga wannan lokacin, ya yanke hukuncin cewa kalaman Donald Trump sun kawo karshen tafiya tsakaninsu.

Donald Trump, wanda ko kadan bai rasa damar sukar tsohon mataimakinsa ba, bai mayar da martani nan take ba.

Sai dai sanarwar ta Mike Pence ta haifar da kaduwa a cikin jam'iyyar, lamarin da ya haifar da ce-ce-ku-ce game da yadda tsohon dan kasuwan zai iya samun cikkaken goyan bayan da ya dace daga ya’an  jam'iyyar Republican.

Donald Trump daga jam'iyyar Republicain
Donald Trump daga jam'iyyar Republicain AP - Andrew Harnik

A cikin makon da ya gabata ne , Nikki Haley, wacce ita ce abokiyar hamayyar Donald Trump ta karshe a zaben fidda gwani, tuni ta ki amincewa da takarar Donald Trump a karkashin inuwar jam’iyyar Republican.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.